Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna.
Ku yi murna tare da Urushalima Ku yi farin ciki tare da ita, Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan! Ku yi murna tare da ita yanzu, Dukanku da kuka yi makoki dominta!
“Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake zaune a Sihiyona, tuduna tsattsarka. Urushalima kuma za ta tsarkaka, Sojojin abokan gāba ba za su ƙara ratsawa ta cikinta ba.
Gama uwarsu ta yi karuwanci. Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya. Gama ta ce, ‘Zan bi samarina Waɗanda suke ba ni ci da sha, Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.’
Ubangiji ya ce, “Kuna tsammani na kori mutanena Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa? To, in haka ne ina takardar kisan auren? Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta Kamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa? A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku, Aka tafi da ku saboda da laifofinku.