Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai, Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.
Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”
Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Ka tarshe ni ko, maƙiyina?” Iliya ya amsa ya ce, “I, na tarshe ka, gama ka ba da kanka ga aikata mugunta a gaban Ubangiji.
Amma da na ga dai ba sa bin gaskiyar bishara sosai, na ce wa Kefas a gaban idon kowa, “Kai da kake Bayahude, in ka bi al'adar al'ummai ba ta Yahudawa ba, yaya kake tilasta wa al'ummai su bi al'adar Yahudawa?
Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”