Saboda haka, ni ma da na kasa daurewa, sai na aika in sami labarin bangaskiyarku, da fatan kada ya zamana mai ruɗin nan ya riga ya ruɗe ku, famarmu kuma yă zama banza.
Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al'ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.
Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
Na ce, “Na yi aiki, amma a banza ne. Na mori ƙarfina, amma ban ƙulla kome ba.” Duk da haka na dogara ga Ubangiji, ya daidaita al'amura, Shi zai sāka mini abin da na yi.