7 Wato kun ga ashe, masu bangaskiya su ne 'ya'yan Ibrahim.
7 Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne.
To, ashe, masu bangaskiya su ne aka yi wa albarka a game da Ibrahim mai bangaskiyar nan.
har saboda mu ma, za a lasafta mana, wato mu da muke gaskatawa da wannan da ya ta da Yesu Ubangijinmu daga matattu,
Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah! Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne, Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.
Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku 'ya'yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi.
Yesu ya ce masa, “Yau kam, ceto ya sauka a gidan nan, tun da yake shi ma ɗan Ibrahim ne.
Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan al'amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato.
Ku sani, an sāki ɗanuwanmu Timoti, da shi ma za mu gan ku, in ya zo da wuri.
Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka'idar nan, wato Isra'ilar gaske ta Allah.