Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Galatiyawa 3:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Wato, Shari'a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A'a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari'a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari'ar nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Galatiyawa 3:21
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari'a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”


Isra'ila kuwa da suka nace da neman hanyar adalcin Allah, suka kasa samunta.


Gama ni ta wurin Shari'a matacce ne ga Shari'a domin in rayu ga Allah.


In kuwa ya zamana, sa'ad da muke neman kuɓuta ga Allah ta wurin Almasihu, an tarar har mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, Almasihu yana hidimar zunubi ne? A'a, ko kusa!


Wato mun soke Shari'a ke nan ta bangaskiyar nan? A'a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.


A'a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa, “Don maganarka tă tabbatar da adalcinka, Ka kuma yi rinjaye in an binciki al'amarinka.”


A'a, ko kusa! To, in da haka ne, ta ƙaƙa Allah zai yi wa duniya shari'a?


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka, suka ce, “Allah ya sawwaƙe!”


Aka zana hidimar Shari'ar Musa, wadda ƙarshenta mutuwa ce, a allunan duwatsu. An bayyana hidimar nan da babbar ɗaukaka, har Isra'ilawa suka kasa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta (ga ta kuwa mai shuɗewa ce).


Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha'anin duniya, duniya kuma ta yar da sha'anina.


Ta wani hali an soke wani umarni ta dā saboda rauninsa da kuma rashin amfaninsa,


don Shari'a ba ta kammala kome ba, ta wani hali kuma an shigo da wani bege wanda yake mafi kyau, ta wurinsa kuwa muke kusatar Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ