Galatiyawa 2:9 - Littafi Mai Tsarki9 sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al'ummai, su kuwa gun masu kaciya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?” Yehonadab ya amsa, “I.” Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.