Haka kuma 'yan'uwana, kun zama matattu ga Shari'a, ta wurin jikin Almasihu, domin ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu ba da amfani ga Allah.
Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda suke a raye, kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.
balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.
Idan mutuwarku tare da Almasihu ta 'yanta ku daga al'adun duniyar nan, me ya sa kuke zama har yanzu kamar ku na duniya ne? Don me kuke bin dokokin da aka yi bisa ga umarnin 'yan adam da koyarwarsu,
An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.
Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari'a la'anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari'a ba, la'ananne ne.”
Ga Yahudawa, sai na zama kamar Bayahude, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda Shari'a take iko da su, sai na zama kamar wanda Shari'a take iko da shi, ko da yake ba Shari'a take iko da ni ba, domin in rinjayi waɗanda Shari'a take iko da su ne.
Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha'anin duniya, duniya kuma ta yar da sha'anina.