wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.
Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na'am da bisharar Almasihu, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.
Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu, Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa. Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’
Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”