Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 9:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Zan raba tsakanin dabbobin Isra'ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra'ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Amma Ubangiji zai raba tsakanin dabbobin Isra’ila da na Masar, saboda kada wata dabbar Isra’ilawa ta mutu.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 9:4
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A wannan rana fa zan keɓe ƙasar Goshen inda jama'ata suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, ta haka ne za ka sani ni Ubangiji ina nan a duniya.


Sa'an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”


Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa'ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala'in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar.


Mutum bai iya ganin ɗan'uwansa ba, ba kuma mutumin da ya iya fita gidansa har kwana uku. Amma akwai haske inda Isra'ilawa suke zaune.


Gobe ne zan aikata al'amarin nan a ƙasar.’ ”


Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al'amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra'ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba.


Sai dai a ƙasar Goshen inda Isra'ilawa suke, ba a yi ƙanƙara ba.


Na hana wa shuke-shukenku ruwa A lokacin da suka fi bukata. Na sa a yi ruwa a wani birni, A wani birni kuwa na hana, Wata gonar ta sami ruwan sama, Amma wadda ba ta samu ba ta bushe.


Sai masu sihiri suka ce wa Fir'auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ