Bayan wannan Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna, suka ce, “Ga abin da Ubangjiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Bar jama'ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.’ ”
Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka je ka sami Fir'auna, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.