Ko tukunyar yumɓu tana iya gardama da magininta, Tukunyar da take daidai da sauran tukwane? Ko yumɓu ya iya tambayar abin da maginin yake yi? Ko tukunya tana iya gunaguni a kan magininta?
Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba. Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala, Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya. Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama'arka.
Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”