Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 8:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Musa ya ce wa Fir'auna, “In ka yarda, a wane lokaci ne kake so in roƙa maka, kai da barorinka da jama'arka domin a kawar da kwaɗin daga gidajenku, a hallakar muku da su, sai dai na cikin Kogin Nilu za a bari?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 8:9
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”


Sa'an nan Iliya ya ce wa annabawan Ba'al, “Ku zaɓi bijimi guda, ku shirya shi da farko, gama kuna da yawa, sa'an nan ku yi kira ga sunan Ba'al ɗinku, amma fa kada ku kunna wuta.”


Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Mutanen da suke tare da kai sun yi yawa da zan ba da Madayanawa a hannunsu, kada ya zama Isra'ilawa su yi mini fāriya, su ce, ‘Ƙarfinmu ne ya cece mu.’


Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa'an nan zai saki jama'ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya.


Fir'auna ya ce, “Gobe ne.” Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu.


Kwana bakwai suka cika bayan da Ubangiji ya bugi Kogin Nilu.


Kwaɗin za su rabu da ku, da kai, da gidanka, da fādawanka, da jama'arka, sai na cikin Nilu kaɗai za a bari.”


Sai Ubangiji ya ce, “Saboda maganarka na gafarta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ