Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 8:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Duk da haka Fir'auna ya taurare zuciyarsa a wannan lokaci kuma, ya ƙi sakin jama'ar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Amma a wannan lokaci ma, Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai kuma bar mutanen suka tafi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 8:32
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Fir'auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita.


Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.


Don me ka bari muka ɓata daga al'amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.


Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa'an nan zai saki jama'ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya.


Ubangiji kuwa ya aikata bisa ga roƙon Musa. Ƙudajen suka rabu da Fir'auna, da fādawansa, da jama'arsa. Ko ƙuda ɗaya bai ragu ba.


Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.


Don me za ku taurare zukatanku kamar yadda Masarawa da Fir'auna suka taurare zukatansu? Sai da Allah ya wahalshe su tukuna kafin su sallami Isra'ilawa su tafi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ