Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 8:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 8:20
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka tafi wurinsa da safe daidai lokacin da ya fita zai tafi Kogin Nilu. Ka jira don ka sadu da shi a bakin Nilu. Ka kuma ɗauki sandan nan wanda ya juye ya zama maciji.


Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka je ka sami Fir'auna, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin Fir'auna, ka ce masa, ‘Ubangiji ya ce ka saki jama'arsa domin su yi masa sujada.


Za su kasa kunne ga muryarka. Sa'an nan kai da dattawan Isra'ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’


Gimbiya, wato 'yar Fir'auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi.


Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.’ ”


Bayan wannan Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna, suka ce, “Ga abin da Ubangjiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Bar jama'ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.’ ”


Sai suka ce, “Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi.”


In kuwa ka ƙi sakin jama'ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama'arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa.


Ya aiko da ƙudaje gare su, suka wahalshe su, Kwaɗi suka lalata filayensu.


Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwari Suka cika dukan ƙasar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ