Zan kawar muku da waɗanda suka zo daga arewa, Zan kori waɗansunsu zuwa cikin hamada. Zan kori sahunsu na gaba zuwa cikin Tekun Gishiri, Zan kori sahunsu na baya, zuwa cikin Bahar Rum. Gawawwakinsu za su yi ɗoyi. Zan yi musu haka saboda dukan abin da suka yi muku.”
“A wannan rana zan ba Gog makabarta a Isra'ila, a kwarin matafiya a gabashin teku. Makabartar za ta kashe hanyar matafiya, gama a can za a binne Gog da dukan rundunar da take tare da shi. Za a kira wurin Hamongog, wato Kwarin Rundunar Gog.
Haka kuwa Ubangiji ya aikata. Ƙudaje masu yawa suka shiga gidan Fir'auna, da gidan fādawansa, da ko'ina a ƙasar Masar. Ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.
Suka kuwa kama bijimin da aka ba su, suka gyara shi suka yi ta kira ga sunan Ba'al tun da safe, har tsakar ranar suna ta cewa, “Ya Ba'al, ka amsa mana!” Amma ba murya, ba kuwa wanda ya amsa. Suka yi ta tsalle a wajen bagaden da suka gina.
Shugabannin birnin Zowan wawaye ne! Mutanen Masar mafi hikima za su ba da gurguwar shawara! Ta ƙaƙa za su iya dosar sarki su faɗa masa, cewa su ne suka gāji masana da sarakuna na dā can?