Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa a gaban Fir'auna. Da sandan ya fāɗi, sai ya zama maciji.
Musa da Haruna kuwa suka yi daidai kamar yadda Ubangiji ya umarta. Sai Haruna ya ta da sandansa sama ya bugi ruwan Nilu a gaban Fir'auna da fādawansa. Dukan ruwan Nilu kuwa ya rikiɗe jini.