Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 7:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Masarawa kuma za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na miƙa hannuna gāba da Masar, don in fito da Isra'ilawa daga tsakiyarsu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Masarawa kuwa za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na miƙa hannuna a kan Masar, na kuma fitar da Isra’ilawa daga gare ta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 7:5
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.”


A wannan rana fa zan keɓe ƙasar Goshen inda jama'ata suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, ta haka ne za ka sani ni Ubangiji ina nan a duniya.


Ubangiji ya ce, za ka sani shi ne Ubangiji ta wurin abin da zan aikata. Zan bugi ruwan Nilu da sandan da yake hannuna, ruwan kuwa zai rikiɗe ya zama jini.


Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.


Domin haka zan miƙa hannuna in bugi Masar da dukan mu'ujizaina waɗanda zan aikata cikinta, sa'an nan zai bar ku ku fita.


Tun daga wannan rana har zuwa gaba, jama'ar Isra'ila za su sani, ni ne Ubangiji Allahnsu.


Zan sanar da sunana mai tsarki a tsakiyar jama'ata, wato Isra'ila, ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji Mai Tsarki a cikin Isra'ila.


Fir'auna ya ce, “Gobe ne.” Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu.


Zan ɗauki fansa saboda sunana mai tsarki, mai girma, wanda aka ɓata a wurin al'ummai, ku kuma kuka ɓata shi a cikinsu. Al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tabbatar da tsarkina a wurinku a kan idonsu.


Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, “ ‘Duba, ina gāba da ke, ya Sidon, Zan bayyana ikona a cikinki, Za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na hukunta ta, Na bayyana tsarkina a cikinta.


Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”


Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci, Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.


Sai masu sihiri suka ce wa Fir'auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”


domin kuma ka sanar da 'ya'yanka da jikokinka yadda na shashantar da Masarawa, na kuma aikata waɗannan mu'ujizai a tsakiyarsu. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.”


Fādawan Fir'auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?”


Sai Musa ya faɗa wa surukinsa dukan abin da Ubangiji ya yi da Fir'auna da Masarawa saboda Isra'ilawa, ya kuma faɗa masa dukan wahalar da suka sha a kan hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.


Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata, Za ka kuwa cece ni da ikonka.


Sa'ad da na mai da ƙasar Masar kufai, In raba ƙasar da abin da take cike da shi, Sa'ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, Daga nan za su sani ni ne Ubangiji.


Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ