Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Ubangiji ya ce, “Ka duba cikin al'umman duniya! Ka gani! Ka yi al'ajabi! Ka yi mamaki! Gama zan yi aiki a kwanakinka, Ko an faɗa maka ba za ka gaskata ba.
Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”
Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.
Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba. Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala, Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya. Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama'arka.
ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.
Masu sihiri kuma na Masar suka yi haka, su ma, ta wurin sihirinsu, don haka zuciyar Fir'auna ta daɗa taurarewa, ya kuwa ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.