Fitowa 7:16 - Littafi Mai Tsarki16 Za ka faɗa wa Fir'auna cewa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya aike ni gare ka da cewa ka saki jama'ar Ubangiji domin su yi masa hidima a jeji. Amma ga shi, har yanzu ba ka yi biyayya ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Sa’an nan ka ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya aiko ni in faɗa maka, Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada a hamada. Amma har yanzu ba ka yi biyayya ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.