Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 7:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Ka tafi wurinsa da safe daidai lokacin da ya fita zai tafi Kogin Nilu. Ka jira don ka sadu da shi a bakin Nilu. Ka kuma ɗauki sandan nan wanda ya juye ya zama maciji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Ka je wurin Fir’auna da safe, yayinda za shi kogi. Ka jira a bakin Nilu don ka sadu da shi, ka ɗauki sandan nan da ya canja zuwa maciji a hannunka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 7:15
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.


Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir'auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa a gaban Fir'auna. Da sandan ya fāɗi, sai ya zama maciji.


Gimbiya, wato 'yar Fir'auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi.


“Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar, Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna, Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir'auna yana da taurin zuciya, ga shi, ya ƙi sakin jama'ar.


Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba, Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ