Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 5:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai suka ce, “Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 5:3
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za su kasa kunne ga muryarka. Sa'an nan kai da dattawan Isra'ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’


Ubangiji Allah ya ce, “Ka tafa hannunka, ka ɗage ƙafarka, sa'an nan ka ce, ‘Kaito, kaito, saboda dukan mugayen abubuwan ƙyama da mutanen Isra'ila suka yi, gama takobi, da yunwa, da annoba za su kashe su.


Dukan abin da Allah na Sama ya umarta, sai a yi shi sosai domin Haikalin Allah na Sama, domin kada ya yi fushi da mulkin sarki da 'ya'yansa.


Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.


A farkon zamansu a can, ba su yi tsoron Ubangiji ba saboda haka Ubangiji ya aika da zakoki a cikinsu, suka karkashe waɗansu daga cikinsu.


Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za ta manne muku, ta cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.


Za ka faɗa wa Fir'auna cewa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya aike ni gare ka da cewa ka saki jama'ar Ubangiji domin su yi masa hidima a jeji. Amma ga shi, har yanzu ba ka yi biyayya ba.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin Fir'auna, ka ce masa, ‘Ubangiji ya ce ka saki jama'arsa domin su yi masa sujada.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.


Za mu yi tafiya kwana uku a jeji kafin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu kamar yadda ya umarce mu.”


Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ