Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 5:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Sai Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangijina, me ya sa ka jawo wa wannan jama'a masifa? Me ya sa ka aike ni?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 5:22
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu, Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni. Na zama abin dariya dukan yini, Kowa yana ta yi mini ba'a.


Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.


In banda kai, wa nake da shi a Sama? Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya?


Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama'ar Isra'ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”


Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”


Dawuda kuwa ya damu ƙwarai gama mutane suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, domin ransu ya ɓace saboda 'ya'yansu mata da maza. Amma Ubangiji Allahnsa ya ƙarfafa shi.


Sai Musa ya ce wa Ubangiji, “Don me ka wahalar da bawanka? Me ya sa ban sami tagomashi a gare ka ba, da ka jibga wahalar dukan mutanen nan a kaina?


Sai Musa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Me zan yi wa jama'an nan? Ga shi, saura kaɗan su jajjefe ni da duwatsu.”


Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?


Sai na ce, “Kaito, kaito, ya Ubangiji Allah, ka ruɗi jama'an nan da Urushalima, da ka ce musu, ‘Za ku zauna lafiya,’ amma ga shi, takobi zai sassare su.”


Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama'an nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ