3 Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule.
3 Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.
Sa'ad da za a tashi daga zango, sai Haruna, tare da 'ya'yansa maza, su shiga cikin alfarwa, su kwance labulen kāriya, su rufe akwatin alkawari da shi.
da akwati da sandunansa, da murfinsa, da labulen ƙofar.
Sa'an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya.
Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.
A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”
“Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa.
“Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi.
Bayan labule na biyu kuma, akwai sashin alfarwa da ake kira Wuri Mafi Tsarki.
Gama tun ranar da na fito da Isra'ilawa ban taɓa zama a cikin ɗaki ba, amma daga alfarwa zuwa alfarwa, daga wannan mazauni kuma zuwa wancan.
a kan alfarwar ta sujada da akwatin alkawari, da murfin da yake bisansa, da dukan kayayyakin da yake cikin alfarwar,
Musa kuma ya ce wa taron jama'ar Isra'ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta,
Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra'ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.