25 Ya kunna fitilun a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
25 ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa.
Ku kuma yi fitilu bakwai, ku sa su a bisa alkukin ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.
Sai walƙiya take ta fitowa daga kursiyin, da ƙararraki, da kuma aradu. A gaban kursiyin kuma fitilu bakwai suna ci, waɗanda suke Ruhohin nan na Allah guda bakwai.
Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa.
faɗa wa Haruna cewa, “Sa'ad da za ka kakkafa fitilun nan bakwai, sai ka kakkafa su yadda za su haskaka sashin gaba.”
Haka kuwa Haruna ya yi. Ya kakkafa fitilun yadda za su haskaka a gaban alkukin, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.