A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.
A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,
A ɗauki kaɗan daga ciki, a niƙa, sa'an nan a ɗiba daga ciki, a ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin alfarwa ta sujada a inda zan sadu da kai. Wannan turare zai zama muku mafi tsarki.
Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da 'ya'yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka'ida har abada ga Isra'ilawa.”
“Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.
A ranar goma ga wata na farko a shekara ta ashirin da biyar ta zamanmu a bautar talala, a shekara ta goma sha huɗu da cin birnin, ikon Ubangiji ya sauko a kaina.