“Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.
Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”
Sa'an nan ka shafa musu mai kamar yadda ka shafa wa mahaifinsu domin su yi mini aiki a matsayin firistoci. Shafa musu man zai sa su zama firistoci din din din dukan zamanansu.”
Sa'ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
Ko kwana biyu ne girgijen ya yi, yana zaune a bisa alfarwar ko wata guda, ko fi, sai Isra'ilawa su yi ta zamansu a zangon, ba za su tashi ba. Amma in ya tashi, sai su kuma su tashi.