Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 40:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 40:13
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka sa wa Haruna, ɗan'uwanka, da 'ya'yansa maza, sa'an nan ka zuba musu mai, ka keɓe su, ka tsarkake su domin su zama firistoci masu yi mini aiki.


Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.


Ku kam, Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya.


To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?


Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak, ba ƙari.


Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.


Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba.


Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.


Sai ka kawo 'ya'yan Haruna maza, ka kuma sa musu taguwoyi.


Ubangiji ya umarci Isra'ilawa su ba firistoci wannan a ranar da aka keɓe su. Wannan hakkinsu ne a dukan zamanansu.


Sai Musa kuma ya kawo 'ya'yan Haruna, maza, ya sa musu zilaiku, ya ɗaura musu ɗamaru, ya sa musu huluna kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.


Ka kuma ɗauki man keɓewa, ka zuba masa a ka domin ka keɓe shi.


Wannan shi ne rabon da aka keɓe wa Haruna da 'ya'yansa maza, daga cikin hadayun da ake yi da wuta ga Ubangiji, tun a ranar da aka keɓe su firistoci na Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ