Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā.
“Idan Fir'auna ya ce muku, ‘Aikata waɗansu al'ajabai don ku nuna isarku,’ sai ka faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa, ya jefa shi ƙasa a gaban Fir'auna. Sandan kuwa zai zama maciji.”
Ka tafi wurinsa da safe daidai lokacin da ya fita zai tafi Kogin Nilu. Ka jira don ka sadu da shi a bakin Nilu. Ka kuma ɗauki sandan nan wanda ya juye ya zama maciji.