Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 4:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 4:10
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah! Ban san abin da zan faɗa ba, Gama ni yaro ne.”


Amma Musa ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Duba, tun da yake Isra'ilawa ba su kasa kunne gare ni ba, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni, ni mutum mai nauyin baki?”


Ko da yake ni bāmi ne a wajen yin magana, a wajen sani kam, ba haka ba ne, mun kuwa bayyana wannan sarai ta kowace hanya a cikin dukan sha'aninmu da ku.


Sai aka karantar da Musa dukan ilimin Masarawa, shi kuwa mutum mai iko ne a cikin magana da ayyukansa.


Musa kuwa ya amsa ya ce, “Ai, ba za su gaskata ni ba, ba kuma za su kasa kunne ga maganata ba, gama za su ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba.’ ”


Don waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa masu ratsa jiki ne, masu ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi ba shi da kwarjini, maganarsa kuma ba wata magana ba ce.”


“Aha! Ashe, kai ne muryar jama'a, Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.


Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi gaban Fir'auna in fito da Isra'ilawa daga cikin Masar?”


Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni?”


Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ