Fitowa 33:3 - Littafi Mai Tsarki3 Ka kama hanya zuwa ƙasa mai yalwar abinci, amma fa ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurin kai, domin kada in hallaka ku a hanya.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Ka haura zuwa ƙasar da take zub da madara da zuma. Amma ba zan tafi tare da ku ba, saboda ku mutane ne masu taurinkai domin mai yiwuwa in hallaka ku a hanya.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.