Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”
Gama Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurin kai. In na yi tafiya tare da ku, nan da nan zan hallaka ku. Domin haka fa, yanzu, ku tuɓe kayan adonku, domin in san abin da zan yi da ku’ ”
Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.
Suka ƙi yin biyayya, Suka manta da dukan abin da ka yi, Suka manta da al'ajaban da ka aikata. Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba, Don su koma cikin bauta a Masar. Amma kai Allah ne mai gafartawa, Kai mai alheri ne, mai ƙauna, Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.
Na ga abubuwanku masu banƙyama, Wato zinace-zinacenku, da haniniya kamar dawakai, Da muguwar sha'awarku ta karuwanci a kan tuddai da filaye, Ya Urushalima, taki ta ƙare! Har yaushe za a tsarkake ki?”