“Da Bezalel da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima, waɗanda Ubangiji ya ba su hikima da basira na sanin yin kowane irin aiki, za su shirya Wuri Mai Tsarki kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’
Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama'a suka yi sujada ga Ubangiji a can.
Tare da shi kuma ga Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan, gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin.
Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.