Fitowa 30:7 - Littafi Mai Tsarki7 Haruna kuwa zai ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kowace safiya lokacin da yake gyarta fitilun. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 “Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.