Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 3:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sa'ad da Ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai Allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, “Musa, Musa.” Musa ya ce, “Ga ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Da Ubangiji ya ga Musa ya matso don yă duba, sai Allah ya yi kira daga cikin ƙaramin itacen ya ce, “Musa! Musa!” Sai Musa ya amsa ya ce, “Ga ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 3:4
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, Da alherin wanda yake zaune a jeji. Bari waɗannan kyautai su sauka a kan Yusufu, A kan wanda yake keɓaɓɓe daga cikin 'yan'uwansa.


Sai ya fāɗi, ya kuma ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”


Ubangiji kuma ya kira Sama'ila sau na uku. Sai kuma Sama'ila ya tashi ya nufi Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Sa'an nan Eli ya gane Ubangiji ne yake kiran yaron,


Ubangiji ya sāke kiran Sama'ila. Sama'ila ya tashi ya tafi wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”


Ubangiji kuwa ya kira Sama'ila. Sama'ila ya ce, “Na'am.”


Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.” Ya amsa ya ce, “Na'am.”


Amma mala'ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai ya ce, “Ga ni.”


Bayan waɗannan al'amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, “Ibrahim!” Sai ya ce, “Ga ni.”


Sau ɗaya Allah ya faɗa, Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.


Sai ya ji wata murya ta ce masa, “Bitrus, tashi, ka yanka ka ci.”


Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala'ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”


Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama'ila! Sama'ila!” Sama'ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.”


Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.”


A can mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba.


Sai Ubangiji ya ce, “Ta haka za su gaskata Ubangiji Allah na kakanninsu ne, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya bayyana gare ka.”


Musa kuwa ya hau bisa dutsen don ya sadu da Allah. Ubangiji ya kira shi daga kan dutsen, ya ce, “Abin da za ka faɗa wa gidan Yakubu, wato Isra'ilawa ke nan,


Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’


Ubangiji ya kirawo Musa, ya yi masa magana daga cikin alfarwa ta sujada, ya ce


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ