Fitowa 3:15 - Littafi Mai Tsarki15 Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |