Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Wata rana, sa'ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato dutsen Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ana nan wata rana Musa yana kiwon tumakin Yetro surukinsa, firist na Midiyan, sai ya bi da tumaki zuwa gefe mai nisa a cikin hamada, har ya zo Horeb, dutsen Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 3:1
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.


Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.


Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamadayane, surukinsa, “Muna kan hanya zuwa wurin da Ubangiji ya ce zai ba mu, ka zo tare da mu, za mu yi maka alheri, gama Ubangiji ya alkawarta zai yi wa Isra'ila alheri.”


“Ku tuna da koyarwar bawana Musa, da dokoki, da umarnai waɗanda na ba shi a kan Dutsen Horeb, domin dukan jama'ar Isra'ila su kiyaye.


Eber, Bakene kuwa, ya ware daga Keniyawa, zuriyar Hobab, surukin Musa, ya kafa alfarwarsa can nesa wajen oak a Za'anannim wanda yake kusa da Kedesh.


Su shirya saboda rana ta uku, gama a kan rana ta uku zan sauko a bisa dutsen Sina'i a gabansu duka.


A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.


Suka ƙera ɗan maraƙi da zinariya a Horeb, Suka yi masa sujada.


da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’


“Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.


Sai Musa ya tashi, shi da baransa Joshuwa, suka tafi, suka hau dutsen Allah.


Musa kuwa ya hau bisa dutsen don ya sadu da Allah. Ubangiji ya kira shi daga kan dutsen, ya ce, “Abin da za ka faɗa wa gidan Yakubu, wato Isra'ilawa ke nan,


Allah kuwa ya ce, “Kada ka matso kusa, ka cire takalminka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne.”


Ana nan waɗansu 'yan mata bakwai, 'ya'yan firist na Madayana suka zo su cika komaye da ruwa domin su shayar da garken mahaifinsu.


Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.


Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi, ka taryi Musa cikin jeji.” Ya kuwa tafi ya tarar da shi a dutsen Allah, ya sumbace shi.


Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da 'yarsa Ziffora.


Lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, Reyuwel, wato Yetro, ya ce musu, “Yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka?”


“To, bayan shekara arba'in, wani mala'ika ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a wani kurmi a jejin Dutsen Sina'i.


Sai Allah ya ce, “Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa ni ne na aike ka. Sa'ad da ka fito da jama'ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan.”


Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.” Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”


Yetro, surukin Musa kuwa, ya miƙa hadaya ta ƙonawa da sadaka ga Allah. Sai Haruna ya zo tare da dattawan Isra'ila duka don su ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.


Da suka tashi daga Refidim, suka shiga jejin Sina'i, sai suka yi zango gaban dutsen.


Domin haka Isra'ilawa suka tuɓe kayan adonsu tun daga dutsen Horeb har zuwa gaba.


Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir.


Sai suka tashi daga dutsen Ubangiji, wato Sinai, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji kuwa ya wuce gabansu don ya nemar musu masauki.


Sai ya tambayi Yesse, “Ko kana da sauran waɗansu 'ya'ya maza?” Yesse ya ce, “Da sauran autan, ga shi kuma, yana wurin kiwon tumaki.” Sama'ila ya ce masa, “Sai ka aika a taho da shi, gama ba zan koma ba, sai ya zo.”


Iliya fa ya tashi daga wurin nan, ya tarar da Elisha ɗan Shafat, yana tare da shanu, garma goma sha biyu. Yana tare da na sha biyun, sai Iliya ya bi ta kusa da shi, ya jefa masa alkyabbarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ