Fitowa 28:9 - Littafi Mai Tsarki9 A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila a kai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 “Ka ɗauki duwatsu biyu masu daraja, ka rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kai အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.
A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.