Fitowa 27:7 - Littafi Mai Tsarki7 Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Za a zura sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefe biyu na bagade a lokacin da ake ɗaukarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.