Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah: ginshiƙi biyu dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan dakali goma daro goma kwatarniya. Bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin Haikalin Ubangiji.