Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”
Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka.
Za su ɗauki alfarwa ta sujada, da labule na ciki da na waje, da murfi na fatun tumaki wanda yake a bisa alfarwar, da kuma labulen ƙofar alfarwa ta sujada,
Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su.
“Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.