A bisa akwatin alkawari kuma akwai kerubobin nan na ɗaukakar Allah, waɗanda suka yi wa murfin akwatin nan laima. Ba za mu iya yin maganar waɗannan abubuwa filla filla ba a yanzu.
Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan'uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.
Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi can ƙuryar Haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama.