Suna bauta wa makamantan abubuwan Sama da kuma ishararsu, kamar yadda Allah ya gargaɗi Musa sa'ad da yake shirin kafa alfarwar nan, da ya ce, “Ka lura fa, ka shirya kome da kome daidai yadda aka nuna maka a kan dutsen.”
Da waɗannan abubuwa ne, ya wajaba a tsarkake makamantan abubuwan da suke a Sama, sai dai ainihin abubuwan Sama za a tsarkake su ne da hadayar da ta fi waɗannan kyau.