Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.
Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’
Kada ku ɓata shari'a, kada ku yi sonzuciya, kada kuma ku karɓi hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanun mai hikima, ya karkatar da maganar adali.
Na san irin zunuban da kuke yi, Da mugayen laifofin da kuka aikata. Kuna wulakanta mutanen kirki, Kuna cin hanci, Kuna hana a yi wa talakawa shari'ar adalci a majalisa.