Fitowa 22:9 - Littafi Mai Tsarki9 “A kowane laifi na cin amana, ko sa ne, ko jaki, ko tunkiya, ko tufa, ko kowane ɓataccen abu, da abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin nan a gaban Allah. Wanda Allah ya ce shi ne da laifi, sai ya biya wa ɗayan ninki biyu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 A kowane rikicin cin amana da zai shiga tsakanin mutum biyu, ko a kan bijimi, ko jaki, ko tunkiya, ko riga, kai, ko a kan kowane irin abin da ya ɓata, da ma abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin a gaban alƙalai. Wanda alƙali ya ce shi ne mai laifi, sai yă biya ɗayan taran da za a yanka, har sau biyu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A duk lokacin da 'yan'uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari'a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari'a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da 'yan'uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi.