Amma fa, ku lura, kada ku yi tunanin banza a zuciyarku, kuna cewa, ‘Ai, shekara ta bakwai, shekarar yafewa ta yi kusa,’ har ku ɗaure wa danginku matalauci fuska, ku ƙi ba shi kome. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.
Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku.
Gama wannan ne kaɗai mayafinsa, da shi zai rufe huntancinsa. Da me zai rufa ya yi barci? Zan amsa masa kuwa in ya yi kuka gare ni, gama cike nake da juyayi.
Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai, Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako. Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka, Gama kullum kakan taimaki masu bukata.