Fitowa 22:21 - Littafi Mai Tsarki21 “Kada ku wulakanta baƙo ko ku zalunce shi, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 “Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”