Kada ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar don kada sa'ad da suke shagulgulan bidi'arsu ga allolinsu, suna miƙa musu hadaya, waninsu ya gayyace ku ku ci abin hadayarsa.
Ku tattara dukan ganimar garin a dandali, ku ƙone garin da dukan ganimar, hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji Allahnku. Garin zai zama kufai har abada, ba za a ƙara gina shi ba.
“Idan aka sami wata, ko wani, daga cikin wani gari da Ubangiji Allahnku yake ba ku, yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku, yana karya alkawarinsa,