Sama'ila ya riga ya rasu, dukan Isra'ilawa kuwa suka yi makoki dominsa, suka binne shi a garinsu, wato Rama. Saul kuma ya riga ya kori masu duba da masu maita daga ƙasar.
Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.
Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu.
Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone a gaban jama'a duka. Da suka yi wa littattafan nan kima, sai suka ga sun kai kuɗi azurfa dubu hamsin.
Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu duba, da masu mafarkai, da matsubbata, ko masu sihiri waɗanda suka ce muku ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.