Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Fitowa 21:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Idan ka sayi bawa Ba'ibrane, zai yi bauta shekara shida, a shekara ta bakwai kuwa, a 'yantar da shi kyauta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Fitowa 21:2
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da kuka 'yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin dukan abin da kuke yi.”


Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya.


Na ce musu, “Da iyakacin ƙoƙarinmu mun fanshi 'yan'uwanmu Yahudawa waɗanda aka sayar wa al'ummai, amma ga shi, kuna tilasta wa 'yan'uwanku su sayar da kansu ga 'yan'uwansu.” Sai suka yi tsit, suka rasa abin da za su ce.


Sai Musa ya umarce su, ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a lokacin da aka ƙayyade na shekarar yafewa, a lokacin Idin Bukkoki,


“A ƙarshen kowace shekara bakwai dole ku yafe dukan basusuwan da kuke bi.


sai dai ko in gari ya riga ya waye. Dole ɓarawon ya yi cikakkiyar ramuwa, in kuwa ba shi da abin biya, a sayar da shi a biya abin da ya satar.


Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku.


Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin.


Matar wani daga cikin ƙungiyar annabawa da ya rasu, ta kai kuka wurin Elisha, ta ce, “Maigidana, baranka, wato mijina, ya rasu, ka kuwa sani shi mai tsoron Ubangiji ne, amma wanda yake binsa bashi ya zo zai kwashe 'ya'yana biyu su zama bayinsa.”


Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa'an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”


Allah ya ba ka daga cikin raɓar sama, Daga cikin ni'imar ƙasa, Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.


Idan yana shi kaɗai aka saye shi, sai ya fita shi kaɗai, idan kuwa yana da aure sa'ad da aka saye shi, sai matarsa ta fita tare da shi.


“Idan mutum ya sayar da 'yarsa kamar baiwa, ba za a 'yanta ta kamar bawa ba.


Idan ba a fanshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, sai a shekara ta hamsin ta murna, a sake shi, shi da 'ya'yansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ