12 “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle, shi ma sai a kashe shi.
12 “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle a kashe shi.
“Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.
Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zare takobi, takobi ne ajalinsa.
“Duk wanda ya kashe mutum, shi ma sai a kashe shi.
Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.” Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.
“Kada ka yi kisankai.
Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan'uwansa.
Idan kuwa bai cika mata wajiban nan uku ba, sai ta fita abinta, ba zai karɓi kome ba.”
“ ‘La'ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’